logo

HAUSA

Amurka ta yi watsi da rayuwa tare da gaza kare hakkin dan Adam na Ukraine

2022-04-14 20:15:08 CMG Hausa

Kwanakin baya kamfanin dillancin labaru na Reuters ya tambayi gwamnatin Biden ta kasar Amurka cewa, me ya sa Amurka ta karbi ‘yan gudun hijira na kasar Ukraine 12 kawai a watan Maris? A wannan rana, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta bayyana cewa, tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine zuwa yanzu, ’yan kasar Ukraine fiye da miliyan 4 da dubu 650 sun tsire daga kasar.

Fadar shugaban kasar Amurka wato White House, ta yi alkawarin karbar ‘yan gudun hijirar kasar Ukraine kusan dubu 100. Amma ‘yan gudun hijira dubu 100 tamkar digo ne a cikin ruwa cikin adadin ‘yan gudun hijirar kasar Ukraine, idan aka kalli hanyoyin karbar ‘yan gudun hijira da kasar Amurka ta tsara, za a ga cewa, Amurka ba ta cika alkawarinta ba.

Binciken da mujallar Forbes ta gudanar ya nuna cewa, idan ‘yan gudun hijira na kasar Ukraine suka samu iznin shiga kasar Amurka, dole ne su tabbatar da cewa, za su koma kasashensu. Amma bisa yanayin rikicin dake faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, wannan wata babbar matsala ga ‘yan gudun hijirar kasar Ukraine su ba da irin wannan tabbaci. (Zainab)