logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun amince da karfafa hadin gwiwa don tinkarar kalubalolin duniya

2022-04-14 10:37:26 CMG Hausa

Kasashen mambobin BRICS sun amince su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da goyon baya ga junansu domin magance kalubaloli masu tarin yawa dake damun kasa da kasa a halin yanzu, wanda ya hada da annobar COVID-19 da farfadowar tattalin arziki.

Kasashen sun yi alkawarin ne a wajen taron tattaunawar BRICS na shekarar 2022 wanda aka gudanar tsakanin Talata zuwa Laraba ta kafar bidiyo.

Ma Zhaoxu, jami’i mai kula da harkokin BRICS, kana mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin wanda ya jagoranci taron, ya ce taron ya samu halartar wakilan kasashen Rasha, da India, da Brazil, da Afrika ta kudu da kuma wakilan kasar Sin daga bangarorin da lamarin ya shafa.

Ya bayyana cewa, yunkurin cimma muradun ajandar dawwamman ci gaba na shekarar 2030, yana fuskantar sabbin kalubaloli, Ma ya ce, ya kamata kasashen BRICS su zurfafa hadin gwiwarsu, da ba da gudunmawar hanyoyin warware matsalolin don tabbatar da adalci, da samar da ingantaccen yanayin ci gaban kasuwannin kasa da kasa, da gina gagarumin tsari na hadin gwiwa don yakar annobar COVID-19, da kuma samar da kwararan matakan da za su kyautata hadin gwiwar kasa da kasa.

Dukkan bangarorin sun amince cewa, ya kamata kasashen BRICS su kara zurfafa goyon bayan junansu da hadin gwiwa a tsakaninsu, kana su bayar da gagarumar gudunmawa domin inganta tsarin shugabanci na kasa da kasa, da bunkasa shirin farfado da tattalin arziki, da aiwatar da ajanda samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, da yaki da annobar COVID-19.(Ahmad)