logo

HAUSA

MOC: Moriyar Juna Ita Ce Jigon Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

2022-04-14 20:07:27 CMG Hausa

Kwanan nan ne, majalisar kula da ciniki tsakanin Amurka da Sin (USCBC) ta fitar da rahoton kayayyakin da Amurka ke fitar zuwa ketare na shekarar 2022. Rahoton ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance muhimmin wurin sayen kayayyakin Amurka, kuma cinikayya da Sin ya samarwa kasar Amurka guraben ayyukan yi masu tarin yawa.

Dangane da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana cewa, kasar Sin ta lura da rahoton da abin ya shafa da Amurka ta fitar, wanda ya bayyana cewa, kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa kasar Sin a shekarar 2021, ya kai wani babban matsayi.

Rahoton ya kuma yi kiyasin cewa, a shekarar 2020, kayayyakin da Amurka ke fitar zuwa kasar Sin, sun taimaka wa kimanin ayyuka 860,000 a kasar, wadanda suka shafi fannonin masana'antu da dama. Bayanai sun nuna cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ta cin moriyar juna da samun nasara tare ne, kuma bangarorin biyu suna da babbar dama ta fadada hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninsu.

A matsayinsu na manyan kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai kyau tsakanin Sin da Amurka, ba kawai tana daga cikin muhimman muradun kasashen biyu da jama'arsu ba ne, har ma tana samar da daidaiton tsarin masana'antu da samar da kayayyaki a duniya, baya ga farfado da tattalin arzikin duniya baki daya.(Ibrahim)