logo

HAUSA

Sin: Ya kamata Amurka ta gaskata batun ‘yancin dan Adam da daidaito da take ta tallatawa.

2022-04-14 19:56:09 CMG Hausa

 

Da yake magana game da yadda ake nuna wariyar launin fata ga kananan kabilu a Amurka, kamar nuna wariya da cin zarafi daga jami’an tsaro, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, kamata ya yi gwamnatin Amurka ta mayar da hankali wajen tunkarar batutuwanta na kare hakkin bil-Adama da tabbatar da daidaiton ‘yanci na kananan kabilu, ciki har da Amurkawa ‘yan asalin Afirka, da gaskata ikirarin da take yi game da ‘yancin dan Adam" da "daidaito" ta yadda dukkan Amurkawa za su ji su kuma gani a kasa.

A ranar 12 ga wata ne, kungiyar nan mai suna National Urban League, ta fitar da rahotonta na shekara-shekara kan halin da Amurkawa ‘yan asalin Afirka suke ciki, wanda ya ce, Amurka ‘yan asalin Afirka na da iyaka a siyasar Amurka. A cikin 2021 kadai, jihohi 20 a fadin kasar sun sake fasalin taswirar gundumomi na mazabun ‘yan majalisa da suka take hakkin Amurkawa ‘yan asalin Afirka da sauran al'ummomi na kada kuri’a. (Ibrahim)