logo

HAUSA

Sin: Bai kamata Amurka ta sanya duniya dandana sakamakon takunkuman kashin kai da ta sanya ba

2022-04-13 20:27:09 CMG Hausa

 

Bisa la'akari da yadda takunkuman kashin kai da Amurka da kawayenta suka kakabawa kasar Rasha suka haifar da matsalar kamfar abinci a duniya, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a taron manema labaru da aka saba yi yau Laraba cewa, takunkuman ba kawai za su kai ga haifar da wani sabon barna wanda kuma ba za a iya daidaita shi ba, har ma za su iya girgiza tsarin tattalin arzikin duniya da ake ciki da kuma mayar da hannun agogo baya, game da kokarin da ake yi na hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa tsawon shekaru da dama. Don haka, ba daidai ba ne, rashin tunani ne, kuma ya saba wa halin kwarai na duniya da daukacin al’ummar dake cikinta. (Ibrahim)