logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Gina Tashar Ciniki Cikin 'Yanci Ta Kasar Sin Da Zai Yi Tasiri A Duniya

2022-04-13 21:33:41 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a gaggauta raya Hainan, zuwa tashar ciniki cikin 'yanci da ke da sigar kasar Sin, da kuma yin tasiri a duniya baki daya.

Xi ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Hainan dake kudancin kasar Sin daga ranar Lahadi zuwa yau Laraba.

Ya kuma bukaci da a zurfafa gyare-gyare da bude kofa a dukkan fannoni, da ci gaba da bunkasa sabbin abubuwa, da daidaitawa tsakanin matakan yaki da annobar COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, da daidaito tsakanin ci gaba da harkar tsaro.

Xi ya ce, Hainan zai zama wani salo na yin gyare-gyare da bude kofa a sabon zamani. (Ibrahim)