logo

HAUSA

Yadda Xi ke ziyarar aiki a kauyen Maona

2022-04-12 16:27:01 CMG Hausa

Jiya Litinin da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kauyen Maona, dake birnin Wuzhishan a lardin Hainan na kasar Sin, domin kara fahimta kan yadda ake inganta sakamakon da aka samu a fannin kawar da talauci a kauyen, da kuma ci gaba da aikin farfado da kauyen.

Cikin shekarun ke nan, an dukufa wajen kyautata muhallin kauyen Maona, domin raya harkokin yawon shakatawa, ta yadda zai kasance abun koyi a fannin neman farfadowar kauyuka a kasar Sin. (Maryam)