logo

HAUSA

An sanya hannu kan ayyuka 36 a yankin ciniki na Hainan

2022-04-12 13:24:59 CMG Hausa

Kimanin ayyuka 36 wadanda jimillar jarinsu ya kai RMB yuan biliyan 13 kwatankwacin dala biliyan 2 aka sanya hannu a ranar Litinin a yankin ciniki mai ‘yanci na lardin Hainan, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

Ayyukan sun shafi wasu fannoni da suka hada da ayyukan sufuri na zamani, da kimiyyar samar da magunguna, da gina masana’antu na zamani, da bunkasa tattalin arziki na zamani, da kasuwannin hannayen jari, da kasuwannin sufurin jiragen sama, da kasuwannin hada-hadar kudi na zamani, da manyan fasahohin aikin gona. An gudanar da bikin sanya hannu kan ayyukan ne a Haikou, babban birnin lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Daga cikin wadannan ayyuka, guda 21 sun shafi fannin kamfanonin harhada magunguna, wanda daya ne daga cikin muhimman ginshikan kamfanonin birnin. Ya zuwa karshen shekarar bara, fannin kamfanonin harhada magunguna a Haikou ta kai RMB yuan biliyan 37.6.

Yanzu haka birnin Haikou ya kasance sansanin gwaji na sana’ar harhada magunguna bisa tsarin fasahohin kirkire-kirkire a yankin ciniki mai ‘yanci na Hainan. (Ahmad)