logo

HAUSA

Firaministan Sin ya bukaci a daidaita yanayin samar da ayyuka da farashi don cigaban tattalin arzikin kasa

2022-04-12 10:51:33 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kiran a daidaita yanayin samar da ayyukan yi, da daidaita tsadar farashi, domin tabbatar da gudanarwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. Li ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya jagoranci wani muhimmin taro game da batun tattalin arzikin kasa.

Da yake tsokaci game da manyan sauye-sauyen dake shafar tattalin arzikin kasar Sin, Li ya bukaci jama’ar kasa, su kasance masu sa lura da zarar an ga wasu alamu na sauyin da ba a yi tsammani ba, da kuma yanayin da zai iya haifar da matsin lamba a yanayin cikin gida da na ketare, kuma a yi kokarin tinkarar sabbin kalubaloli.

Li ya kuma jaddada muhimmancin dagewa wajen samar da muhimman kayayyakin bukatun yau da kullum ga mutanen da ke fuskantar annobar COVID-19, kuma akwai bukatar a kara himma da kwazo don biyan bukatun al’umma ta fannin kiwon lafiya. (Ahmad)