logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Tabbatar Da Zaman Lafiya A Ukraine Ta Hanyar Daukar Hakikanin Matakai Maimakon Sanya Takunkumi

2022-04-11 20:53:07 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bukaci kasar Amurka da ta dauki matakai na hakika, don samar da zaman lafiya a halin da ake ciki a kasar Ukraine, maimakon samun moriya daga tayar da hargitsi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a Litinin, lokacin da aka tambaye shi game da takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar Rasha.

Zhao ya kuma yi Allah-wadai da yadda Amurka ke amfani da takunkumi a matsayin wani makami don kiyaye matsayinta na nuna danniya da samun moriya ba bisa ka'ida ba.

Jami’in na kasar Sin ya nanata matsayin kasar Sin kan wannan batu, yana mai nanata cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce kadai madaidaiciyar hanyar warware rikicin Ukraine.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan bangarorin Rasha da Ukraine, don shawo kan matsaloli da kuma ci gaba da yin shawarwari. Haka kuma, muna maraba da goyon bayan kasashen duniya, kan shawarwarin zaman lafiya tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Muna karfafa gwiwar bangarorin biyu, da su ci gaba da sa kaimi wajen yin shawarwarin da kokarin samar da sakamako da zaman lafiya. (Ibrahim yaya)