logo

HAUSA

Sin ta fitar da tsarin kafa kasuwar cikin gida ta bai daya

2022-04-11 14:12:37 CMG Hausa

Mahukuntan kasar Sin sun fitar da tsarin gaggauta kafa kasuwar cikin gida ta bai daya, wadda za ta kasance mai inganci, mai biyayya ga dokoki, da daidaito, kuma bisa tsarin gogayya mai nagarta.

Tsarin wanda kwamitin kolin JKS, tare da majalissar gudanarwar kasar Sin suka yi hadin gwiwar fitarwa, na da nufin bunkasa inganci, da fadadar kasuwar cinikayya ta cikin gidan kasar Sin. Ana kuma fatan tsarin zai samar da daidaito, da adalci, da bayyana komai a fili, da damar iya hasashen yanayin hada hadar cinikayya, da rage kudaden gudanar da cinikayya.

Kari kan hakan, tsarin zai bunkasa kirkire-kirkiren kimiyya, da daga matsayin masana’antu, da bullo da sabbin damammaki na shigar masu takarar cinikayya na kasa da kasa, da hadin gwiwa a kasuwar kasar.

Kaza lika, za a kara azama wajen inganta tsarin hade sassan dokokin mallakar fasaha, da aiwatar da tsarin samar da damar shiga kasuwar bai daya, da kara kyautata hadadden tsarin samarwa al’umma lamuni.  (Saminu)