logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 11.36

2022-04-11 10:23:38 CMG Hausa

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai miliyan 11,363,738 ya zuwa yammacin Lahadin da ta gabata, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ne ta sanar da hakan.

A cewar kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, yawan mutanen da cutar ta kashe a fadin nahiyar ya kai 251,551 sannan majinyata 10,725,904 ne suka warke bayan fama da cutar kawo yanzu.

Afrika CDC ta ce, kasashen Afrika ta kudu, da Morocco, da Tunisia, da Masar, da kuma kasar Libya, suna daga cikin kasashe mafiya fama da masu dauke da cutar a nahiyar.

Sannan Afrika ta kudu ce ta fi kowace kasa yawan adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika, inda take da mutane 3,731,247, sai Morocco dake bi mata baya da adadin mutane 1,163,962 da suka kamu da cutar, ya zuwa yammacin ranar Lahadin.

Game da adadin masu fama da cutar, kudancin Afrika ne shiyyar da ta fi yawan masu kamuwa da cutar, sai shiyyar arewaci da gabashin Afrika dake bi mata baya, yayin da shiyyar tsakiyar Afrika ke da karancin adadin masu kamuwa da cutar a nahiyar, a cewar Afrika CDC. (Ahmad)