logo

HAUSA

Saudiyya za ta karbi miliyan guda daga ciki da wajen kasar a hajjin bana

2022-04-10 16:48:00 CMG Hausa

 

Ma’aikatar kula da ayyukan Hajji da Umrah ta kasar Saudi Arabiyya ta sanar a ranar 9 ga wata da cewa, za ta baiwa maniyyata miliyan 1 daga ciki da wajen kasar damar halartar aikin hajjin bana a Makka.

Sanarwar ta ce, matakin zai baiwa musulmai masu yawa daga sassan daban daban na duniya damar sauke farali na ayyukan ibada a kasa mai tsarki.

Sai dai ma’aikatar ta ce, dole ne maniyyatan aikin hajjin na bana su kasance ‘yan kasa da shekaru 65 da haihuwa, kuma su tabbatar sun kammala karbar cikakkun alluran rigakafin cutar annobar  numfashi ta COVID-19.

Ta kara da cewa, dole ne maniyyata aikin hajjin na kasashen waje su gudanar da gwajin cutar a cikin sa’o’i 72 gabanin su tashi zuwa kasar Saudiyyan.

Wannan shi ne karon farko da ake sa ran baiwa maniyyata daga kasashen waje damar gudanar da ayyukan hajjin a Saudiyya, yayin da a cikin shekaru biyu da suka gabata, an baiwa ‘yan tsirarun mutane daga cikin gidan kasar damar halartar aikin hajjin a matsayin matakan dakile yaduwar annobar COVID-19.

A cewar ma’aikatar, a shekarar 2021, birnin Makka ya karbi mahajjata 60,000 ne kacha, sabanin sama da mutane miliyan 2.5 da suka halarci aikin hajjin a shekarar 2019.(Ahmad)