logo

HAUSA

Muhimman kalaman Xi Jinping a yayin taron yabawa wadanda suka taka rawar gani yayin wasannin Olympics na lokacin sanyi da na nakasassu na lokacin sanyi na birnin Beijing

2022-04-09 20:33:43 CMG Hausa

A ranar 8 ga wata, an shirya taron nuna yabo ga wadanda suka taka rawar gani yayin wasannin Olympics na lokacin sanyi da na nakasassu na lokacin sanyi na birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya ce, “An shirya bukukuwan budewa da na rufewa guda hudu masu kayatarwa, inda aka nuna taken al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam a dukkan lokacin, al'adun kasar Sin da wasannin  kankara suna dacewa da juna, wanda ke nuna kyawawan yanayi, al’adu da wasanni.”

Xi Jinping ya ce, “wasannin kankara na taimakawa jama’a wajen samun wadata da farfado da harkokin da suka shafi karkara.”

Xi Jinping ya ce, “Matakan shawo kan cutar COVID-19 sun jure jarrabawa, har sun samar da fasahohi masu amfani ga yaki da cutar a duniya, da kuma gudanar da manyan bukukuwan kasa da kasa.”

Xi Jinping ya ce, “Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta aike da babbar murya ta zamani ‘mu hadu gaba domin amfanin gaba’ ga duniya.”