logo

HAUSA

Tawagar jami’an lafiya na kasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin lafiya a kasar saliyo

2022-04-09 17:12:57 CMG Hausa

Tawagar jami’an lafiya na kasar Sin dake aiki a Saliyo, ta samar da gudunmuwar kayayyakin lafiya ga asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, domin bunkasa hidimomin kiwon lafiya.

Shugaban tawagar Zhou Xi, ya ce kayyakin sun hada da rukunoni 24 na magungunan da ake bukata sosai da sama da nau’o’i 30 na kayayyakin aiki, wadanda za su taimaka wajen cike gibin karancin kayayyakin lafiya dake akwai a asibitin.

A cewar Zhou Xi, asibitin, wanda a nan ne tawagar ta kasar Sin ke aiki, ya dade yana fuskantar karancin kayayyaki da wutar lantarki da ruwa, wadanda ke zaman barazana ga marasa lafiya da ma ma’aikata.

Ya ce duk da annobar COVID-19 da wasu tarin kalubale, daga farkon bana zuwa yanzu, tawagar ta yi nasarar gudanar da tiyata sama da 40, yana mai cewa, jami’an tawagar za su dage wajen musayar dabaru da takwarorinsu na Saliyo da kuma ci gaba da kulawa da marasa lafiya na kasar. (Fa’iza Mustapha)