logo

HAUSA

​Rundunar sojin Nijeriya: Babban kwamandan BH ya mika wuya

2022-04-08 10:15:18 CMG Hausa

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar a jiya cewa, wani babban kwamandan kungiyar masu tsatssauran ra’ayi ta BH, ya mika wuya ga sojojinta yayin da ake tsaka da kai wa kungiyar farmaki a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin Bernard Onyeku, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, kwamandan na BH mai suna Saleh Mustapha, shi ne shugaban kungiyar a yankin Bama, daya daga cikin wuraren da suka fi fama da hare-hare a jihar Borno, dake arewa maso gabashin kasar.

Bernard Onyeku ya kara da cewa, Mustaphan ya mika wuya ga sojoji ne a ranar Talata, yana mai bayyana cewa, tun daga ranar 25 ga watan Maris, ayyukan soji kan ‘yan ta’adda ya tsananta a yankin. (Fa’iza Mustapha)