logo

HAUSA

WHO: Ya yiwu fiye da 2/3 na mutanen kasashen Afirka sun taba kamuwa da COVID-19

2022-04-08 13:38:12 CMG Hausa

Matshidiso Moeti darekta mai kula da yankin Afirka ta hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana a jiya Alhamis a Brazzaville na jamhuriyar Congo cewa, ainihin adadin mutanen kasashen Afirka da suka taba kamuwa da cutar COVID-19 ya zarce jimillar da aka sanar sosai. A cewarta akwai yiwuwar fiye da kashi 2 cikin kashi 3 na daukacin al’ummar nahiyar sun riga sun kamu da cutar.

An ce, hukumar WHO ta tabbatar da hakan ne, bisa nazari kan rahotanni fiye da 150 da aka gabatar tsakanin watan Janairun shekarar 2020 da watan Disamban shekarar 2021.

Madam Moeti ta kara da cewa, nazarin da aka yi ya nuna cewa har yanzu cutar COVID-19 na ci gaba da bazuwa, kana za ta iya sauya salo zuwa wani nau’i mai kisa sosai, saboda haka ya zama wajibi a ci gaba da kokarin gwajin kwayoyin cutar, da sa ido kan wadanda suka taba cudanya da mutanen da suka kamu da cutar. Jami’ar ta sake nanata muhimmancin karbar allurar rigakafi, ta kuma yi kira ga kasashe daban daban dake nahiyar Afirka da su kara saurin gudanar da aikin yi wa jama’arsu allurar. (Bello Wang)