logo

HAUSA

Sin ta bukaci a gaggauta soke shirin Nancy Pelosi na ziyartar Taiwan

2022-04-07 20:57:10 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na gargadin kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi, da ta gaggauta janye shirin ta na ziyartar yankin Taiwan, kuma idan har jami’ar ta yi gaban kan ta wajen aiwatar da hakan, Sin za ta dauki kwakkwaran mataki na kare ikon mulkin kai, da martabar yankunan ta, kuma Amurka ce za ta dauki alhakin duk abun da ya biyo baya.

Jami’in ya kara da cewa, ya kamata Amurka ta martaba bangaren ta na sanarwa 3 da sassan 2 suka sanyawa hannu, game da amincewa da manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. (Saminu)