logo

HAUSA

An yankewa tsohon shugaban Burkina Faso hukuncin daurin rai da rai

2022-04-06 20:35:53 CMG Hausa

Wata kotun soji a Burkina Faso, ta yanke wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai da rai, bayan samun sa da laifin halaka wanda ya gada, wato shugaba Thomas Sankara, yayin juyin mulkin kasar na shekarar 1987.

Kaza lika, yayin zaman kotun sojin na Larabar nan, ta yankewa manyan jami’an tsaro a gwamnatin Compaore, Janar Gilbert Diendere, da Hyacinthe Kafando hukuncin daurin rai da rai.  (Saminu)