logo

HAUSA

Sin ta yi tir da matakin Amurka na amincewa da sayarwa Taiwan makamai

2022-04-06 21:34:51 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasar sa ta yi Allah wadai da matakin Amurka, na amincewa ta sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai, wadanda darajar su ta kai dala miliyan 95. Kuma Sin din ta sha alwashin daukar matakai na hakika, domin kare ikon mulkin kai da moriyar tsaron kasar ta.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, ya ce sayarwa Taiwan makamai, mataki ne na keta ikon mulkin kai, da tsaro da moriyar ci gaban Sin, yana kuma gurgunta alakar Sin da Amurka, tare da lalata yanayin zaman lafiya da daidaito a zirin Taiwan.

Daga nan sai jami’in ya yi kira ga Amurka, da ta rungumi manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi 3 da sassan biyu suka amincewa, ta kuma yi watsi da batun cinikayyar makamai, da duk wata cudanyar ayyukan soji tsakanin ta da Taiwan.  (Saminu)