logo

HAUSA

Xi da takwaransa na kasar Armeniya sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu

2022-04-06 14:18:13 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Armeniya Vahagn Khachaturya, suka yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, yana son yin aiki tare da shugaba Vahagn Khachaturya, wajen amfani da bikin cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama, ta inganta dangantakar da hadin gwiwar a tsakanin Sin da Armenia a fannoni daban daban, don samun sakamako mai kyau, don samun moriyar juna, ta yadda hakan zai amfanawa kasashen biyu da al’ummunsu.

A nasa bangare, shugaba Khachaturya ya bayyana cewa, yana son yin aiki tare da shugaba Xi Jinping, domin tabbatar da dorewar ci gaban dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen Armenia da Sin, da kuma amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Ibrahim)