logo

HAUSA

An samu daidaituwar ayyukan sufurin jiragen kasa da aika sakonni a lokacin bikin Qingming na kasar Sin

2022-04-06 14:42:23 CMG Hausa

Kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya yi jigilar jimillar fasinjoji miliyan 8.51 a lokacin hutun bikin Qingming, wato share kaburburan magabata na kasar Sin, kuma harkokin sufurin jiragen kasan yana gudana yadda ya kamata.

Sannan bisa alkaluman da hukumar aika sakonni ta kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Afrilu, an samu kyakkyawan yanayin ayyukan kamfanonin aika sakonnin kayayyaki, inda aka aika jimillar sakonnin kayayyaki miliyan 660, wato an samu raguwar aika sakonnin kayayyaki da kashi 13.3% bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2021, kuma idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020, an samu karin kashi 24.1%, inda aka aika jimillar sakonni miliyan 690, kasa da kashi 12.8 bisa 100 a bisa da na makamancin lokacin shekarar 2021, da kuma karuwar kashi 27.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2020. (Ahmad Fagam)