logo

HAUSA

Xi ya taya Aleksandar Vucic murnar sake lashe zaben shugaban kasar Serbia

2022-04-05 21:09:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Aleksandar Vucic, sakamakon sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Serbia.

A sakonsa, Xi ya bayyana cewa, cikin shekarun baya-bayan nan, hadin gwiwar Sin da Serbia ya samu ci gaba sosai, inda bangarorin biyu suke da aminci mai karfi ta fuskar siyasa da kuma hadin gwiwa mai inganci.

Ya kara da cewa, a shirye yake ya hada hannu da shugaba Vucic, wajen karfafa tuntuba da aminci a tsakaninsu, tare da fadadawa da zurfafa hadin gwiwar moiyar juna a bangarori daban-daban tsakanin kasashen biyu, da ma kyautata huldarsu don samun sabbin nasarori ta yadda za su amfanawa kasashen biyu da jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)