logo

HAUSA

An gudanar da zanga-zangar adawa a Madrid game da tsoma bakin kungiyar tsaro ta NATO a rikicin Ukraine

2022-04-04 16:28:29 cri

Daruruwan mutane ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Madrid na kasar Sifaniya jiya Lahadi, domin nuna adawa da rikicin dake faruwa a kasar Ukraine, da kuma yadda kungiyar tsaro ta NATO ke tsoma baki a lamarin.

Masu zanga-zangar, wanda babban taron da ya kunshi kungiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya, sun hallara a gaban tashar jirgin kasa ta Puerta de Atocha, inda suka yi tattaki zuwa ma'aikatar harkokin wajen kasar

A cewar Lorena Cabrera, wakilin kungiyoyin dake yaki da ’yan jari hujja, da kuma shugabannin kungiyoyin da dama, bai dace kasar Sifaniya ta sake mika wuya ga matsin lamba na kungiyar tsaro ta NATO ba, saboda tuni tasirin goyon bayan rikicin, ya yi matikar shafar sassa daban-daban.

A cewar Luis Arevalo, daya daga cikin masu zanga-zangar, muna son zaman lafiya a kasar Ukraine da ma dukkan kasashe. Kana muna adawa da yadda kasashen Turai ke kara shiga cikin yakin soji dake faruwa a kasar Ukraine, saboda suna yin hakan ne bisa muradun Amurka.

Alkaluman da cibiyar masarautar ElCano ta fitar a ranar Juma'a na nuna cewa, kashi 52 cikin 100 na al’ummar kasar Sifaniya, suna goyon bayan shiga tsakani, idan aka kwatanta da kashi 48 cikin 100 dake adawa da hakan.

Darektan cibiyar sa ido kan manufofin kasar Sin ta kasar Sifaniya Xulio Rios, ya bayyana cewa, bai kamata kungiyar Tarayyar Turai EU, ta shiga matakai marasa dacewa da Washington ke tsarawa ba, domin kiyaye martabarta.(Ibrahim)