logo

HAUSA

An kashe mutane 20 a harin ta’addanci a mahakar zinaren kasar Burkina Faso

2022-04-03 20:32:35 CMG Hausa

Fararen hula a kalla 20 aka kashe, kana an raunata wasu dama, a wani hari da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka kaddamar a wajen hakar zinare dake arewacin kasar Burkina Faso a ranar Asabar, kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai da dama suka bayyana.

A cewar wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaye sunansa, wasu ‘yan bindiga kan babura ne suka kaddamar da harin a mahakar zinare ta Kougdiguin.

Shi ma wani mazaunin yankin yace, akwai mata da kananan yara daga cikin wadanda harin ya rutsa dasu, yayin da wani jami’in kiwon lafiya a wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba ya ce, an kwantar da mutane 10 domin yi musu jinya sakamakon raunukan da suka samu sannan yace akwai wasu dake karbar kulawa a sauran asibitoci.

Harin ya zo ne kasa da wata guda bayan wani makamancinsa da aka kaddamar a wata mahakar zinaren da ke kasar, inda aka kashe mutane 11.(Ahmad)