logo

HAUSA

Masana: Kasashen dake bin shawarar ziri daya da hanya daya sun zamanto cibiyoyin bunkasa tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwar moriyar juna

2022-04-02 16:00:47 CMG Hausa

Kwararrun masana tattalin arzikin kasar Pakistan, da masu gabatar da jawabai daga kasashe daban-daban da suka halarci taron kwanaki biyu na tattauna al’amurran tsaro a Islamabad sun bayyana cewa, kasashen da suka shiga ‘shawarar ziri daya da hanya daya’ BRI, wanda kasar Sin ta gabatar, suna ci gaba da kasancewa wasu manyan cibiyoyin bunkasar tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwar moriya juna wanda shawarar ke dauke da su.

A yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Ashfaque Hasan Khan, babban mai sharhi kan tattalin arziki, kana mamban majalisar gudanarwar tattalin arzikin kasar Pakistan, yace, kasar Pakistan daya ce daga cikin misalai na wadanda suka yi matukar amfana daga shawarar BRI ta hanyar dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na Sin da Pakistan (CPEC), wanda ba kawai ya taimaka wajen bunkasar cigaban ababen more rayuwa ba ne, har ma ya ba da damar share hanyar bunkasar masana’antun kasar.

Da yake jawabi a taron tsaron na Islamabad, shugaban kasuwannin musayar kudade na Pakistan, Shamshad Akhtar ya ce, shawarar BRI tana da matukar muhimmanci ga Pakistan da sauran kasashen da suka shiga shawarar, don haka duk wani sauyin yanayin tsaron duniya ba lallai ne ya haifar da mummunan tasiri ba.(Ahmad)