logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci kasa da kasa su tallafawa Somalia a fannin tsaro

2022-04-01 10:25:22 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya bukaci kasa da kasa su ci gaba da tallafawa kasar Somaliya a fannin tsaro.

Yace, a halin yanzu, al’amurran tsaro a kasar Somaliya na ci gaba da fuskantar kalubaloli, lamarin da ya zama tilas ga kasashen duniya su ci gaba da tallafawa Somaliyar domin tinkarar matsalolin tsaron, jakadan ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da jawabi bayan kwamitin sulhun MDD ya amince da wani kudiri na neman sauya fasalin shirin tawagar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayya Afrika a Somaliya zuwa tawagar wucin gadi ta kungiyar tarayyar Afrika a Somalia wato (ATMIS).

Dai ya ce, kasar Sin tana goyon ci gaban da kwamitin sulhun MDD ya samu game da shirin ATMIS, kana tana fatan dukkan bangarorin da lamarin ya shafa za su karfafa hadin gwiwa don yin aiki tare wajen aiwatar da shirin na ATMIS, sannan su yi aiki tare da gwamnatin Somaliya domin taimaka mata wajen sauke muhimmin nauyin dake bisa wuyanta na tabbatar da tsaron kasa.

A ranar Alhamis, kwamitin sulhun MDD ya kada kuri’ar amincewa da kudirin sauya fasalin tawagar na AU a Somalia da kuma aiwatar da shirin janye dakarun tawagar wanzar da tsaro ta AU daga kasar sannu a hankali.(Ahmad)