logo

HAUSA

Wang Yi ya jaddada matsayin kasar Sin kan batun kasar Ukraine

2022-04-01 13:44:21 CMG Hausa

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a jiya Alhamis a birnin Tunxi dake lardin Anhui na gabashin kasar Sin cewa, kasar Sin ta taka rawar da ta dace kan batun kasar Ukraine.

Minista Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karin haske, kan matsayin kasar Sin game da batun kasar Ukraine, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan taron ministocin harkokin wajen kasashen dake makwabtaka da kasar Afghanistan karo na uku, da kuma taron ministocin harkokin waje na farko a tsakanin kasashen dake makwabtaka da Afghanistan da gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan.

Kasar Sin dai ta yi imanin cewa, tattaunawa da shawarwari, ita ce hanya daya tilo mafi dacewa wajen warware batun kasar Ukraine. Ya kara da cewa, kasar Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta tare da goyon bayan tattaunawa kai tsaye tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.(Ibrahim)