logo

HAUSA

Kalaman Wang Yi game da batun amincewa da gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan ta hanyar diplomasiyya

2022-04-01 14:22:38 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron manema labarai, bayan da ya jagoranci taron tattaunawa na ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan Afghanistan karo na uku, kana taron tattaunawa na farko tsakanin ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan Afghanistan da gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan a jiya Alhamis a birnin Tunxi, na lardin Anhui.

Da aka tambaye shi, ko kasar Sin za ta amince da gwamnatin rikon kwaryar Taliban ta kasar Afghanisatan? Wang yi ya bayyana cewa, al’ummar kasar Afghanisatan suna da ‘yancin rayuwa cikin kwanciyar hankali, kana kasar Afghanistan tana da ‘yancin tsayawa a matsayin kasa mai cikakken iko a duniya.

Wang Yi ya ce, gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan tun bayan kafuwarta ta yi kokari matuka tare da cimma muhimmin sakamako wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ma tafiyar da harkokin kasar. Ya ce, an lura cewa, kasa da kasa, da suka hada da makwabtan kasashe, suna bada kwarin gwiwa ga gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan da ta yi namijin kokari wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa, da kafa tsarin shugabanci da zai shafi kowane bangare, kuma a tabbatar da kiyaye hakkokin mata da kananan yara wajen basu guraben aiki da ilmi. Musamman, ta bayar da kwarin gwiwa wajen samar da muhimman sakamako wajen kawar da ayyukan ta’addanci. Wang Yi ya ce, har yanzu, akwai sauran kokarin da ake bukata domin warware matsalolin da aka ambata tun da farko. Amma an yi amanna cewa, batun amincewa da gwamnatin Afghanistan ta hanyar diplomasiyya zai tabbata, idan ta kara amsa bukatun bangarori daban daban. Muna fatan gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan zata dauki ingantattu da kuma kwararan matakai dangane da wannan batu.

Wang Yi ya kuma yi karin bayani kan takardu guda 2 da aka zartas a yayin tarukan 2, wadanda suka bayyana matsayin bai daya da kasashe makwabtan Afghanistan suka cimma a siyasance, sun kuma tsai da kudurin mara wa Afghanistan baya a fannonin ba da agajin jin kai, tuntubar juna da cudanya, tattalin arziki da ciniki, ci gaban aikin noma, makamashi da wutar lantarki da kara karfin kasa. (Ahmad)