logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya ba da jawabi a rubuce ga taron ministocin harkokin wajen kasashe masu makwabtaka da Afghanistan

2022-03-31 14:09:26 CMG Hausa

Yau Alhamis 31 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a rubuce, ga taro karo na uku na ministocin harkokin wajen kasashen masu makwabtaka da Afghanistan, inda ya nuna cewa, kasar Afghanistan na fama da wahalhalu, tana jiran farfadowa daga dukkan fannoni. Afghanistan da sauran kasashe masu halartar taron makwabta abokai ne, wadanda ke da makomar bai daya. Samun kasar Afghanistan mai zaman lafiya, da zaman karko, da cigaba, da ma wadata, ba burin al’ummun kasar kadai ba ne, domin kuwa hakan ya dace da muradun kasashen dake yankin, da ma sauran kasashen duniya.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ko da yaushe kasar Sin na mutunta ikon mulkin kasar Afghanistan, da ’yancin kanta, da ma cikakkun yankunanta. Kana Sin na dukufa kan yunkurin Afghanistan na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa.

A karshe dai, Shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata kasashe makwabtan Afghanistan su yi iyakacin kokari, wajen cimma ra’ayin bai daya da hadin kansu, domin mara wa ’yan kasar baya wajen raya kyakkyawar makoma. (Kande Gao)