logo

HAUSA

Ghana za ta fara samar da rigakafin COVID-19 daga shekarar 2024

2022-03-31 09:50:02 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya ce kasarsa za ta fara samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 a cikin gida tun daga watan Janairun shekarar 2024.

Shugaba Akufo-Addo ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, lokacin da yake gabatar da jawabi game da yanayin da kasar ke ciki a bana, gaban taron majalissar dokokin kasar. Ya ce yadda manyan kasashen duniya suka mallake rigakafin da suke samarwa a cikin kasashensu, ya tabbatar da bukatar samar da rigakafin a Ghana.

Shugaban na Ghana, ya ce nan ba da jimawa ba, zai gabatar da kudurin neman amincewar majalissar na kafa cibiyar sarrafa rigakafin na COVID-19.

Ya ce bazuwar wannan annoba ya sake fayyace matsalolin dake addabar kasar, wadanda suka fadada damuwar da al’ummar kasar ke ciki. Don haka, bisa burin gwamnatinsa na kara kyautata tsarin kiwon lafiyar al’ummar Ghana, shugaba Akufo-Addo ya sha alwashin gina sabbin asibitoci 111 a sassan kasar daban daban, domin biyan bukatun al’umma.

A ranar Lahadin karshen makon jiya ne shugaban na Ghana, ya bayyana dage akasarin matakan yaki da COVID-19 da kasar ke aiwatarwa, ciki har da bude kan iyakokin kasar na ruwa da kasa, da dage dokar hana taruwar jama’a, bayan da bazuwar cutar ta ragu, kuma aka samu karin masu karbar rigakafin cutar a Ghana.   (Saminu)