logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwaransa na Rasha

2022-03-30 20:38:21 CMG Hausa

 

Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov a lardin Anhui, wanda ya zo kasar Sin don halartar taron ministocin harkokin wajen kasashe makwaftan kasar Afghanistan karo na uku.

Wang Yi ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, Sin tana goyon bayan kasashen Rasha da Ukraine, da su ci gaba da shawarwarin zaman lafiya don shawo kan matsaloli, da goyon bayan kyakkyawan sakamakon da aka cimma a shawarwarin, kana tana goyon bayan kwantar da hankula a kasar cikin sauri.

A nasa jawabin Sergei Lavrov ya ce, kasar Rasha ta kuduri aniyar kawo karshen tashin hankalin, kuma za ta ci gaba da tattaunawa da kasar Ukraine. (Ibrahim)