logo

HAUSA

Ma'aikatar wajen kasar Sin ta mayar da martani game da barkewar tashin hankali a wasu sassan Sudan ta Kudu

2022-03-30 19:28:34 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, Larabar nan ya shirya taron manema labarai na yau da kullum. Kuma wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, a baya-bayan nan an samu tashe-tashen hankula a wasu sassan Sudan ta Kudu. Shin mene ne ra’ayin kasar Sin?

Wang Wenbin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu, an samu gagarumin ci gaba a yunkurin samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, wanda kuma ya dace da muhimman muradun al'ummar kasar. Kasar Sin tana kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su mutunta nasarorin da aka samu na zaman lafiya, da ci gaba da warware sabanin ra'ayi ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Yayin da yake karin haske kan rikicin dake faruwa tsakanin kasashen Rasha da Ukraine kuwa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon baya tare da karfafa dukkan matakai na diflomasiyya, da za su taimaka wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana.

Haka kuma, Wang Wenbin ya ce, a ko da yaushe gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya. (Ibrahim)