logo

HAUSA

Wani jirgin ruwan yakin Rasha ya nutse sakamakon harin da aka kai masa

2022-03-28 09:58:26 CMG Hausa

A ran 24 ga watan Maris, rundunar sojin Ukraine ta sanar da cewa, sojinta sun kai hari kan wani jirgin ruwan yaki na Orsk na kasar Rasha da aka jibge a tashar teku ta Berdyansk ta kasar Ukraine. Har yanzu wannan tashar teku tana hannun sojin Rasha. Sai dai, wannan jirgin ruwan yaki na Orsk na Rasha ya nutse cikin ruwa. (Sanusi Chen)