logo

HAUSA

Su ne masu tayar da fitina ta bayan fage

2022-03-28 19:29:36 CRI

“Wannan mutumin wato shugaban Rasha Vladimir Putin, ba zai ci gaba da kasancewa a kan mulki ba.” Shugaban kasar Amurka Joe Biden ne, ya furta haka a ranar 26 ga Maris, agogon kasar Poland, a wani jawabi da ya yi kan rikicin kasashen Rasha da Ukraine. Wannan jimla ta fallasa ainihin manufar takala ta Washington, da nufin ruguza kasar Rasha, da ma hambarar da gwamnatin Rasha, da kuma taimakawa Amurka ta mamaye duniya.

Rikicin kasashen Rasha da Ukraine shi ne misali na baya-bayan masu tarin yawa na Amurka da ke neman muradun siyasa ta hanyar ruruta tashe-tashen hankula a wasu kasashe ko kuma kaddamar da yaki kai tsaye. Wasu alkaluman kididdiga da ba a tantance su ba, sun nuna cewa, tun bayan ayyana ‘yancin kai a shekarar 1776, a cikin fiye da shekaru 240 na tarihi, Amurka ba ta shiga yake-yake a cikin kasa da shekaru 20 ba, daga karshen yakin duniya na biyu a shekarar 1945 zuwa 2001, Kasashe da yankuna 153 a duniya, sun fuskanci tashe-tashen hankula 248, kuma 201 daga cikinsu, Amurka ce ta tayar da su, wanda ya kai kusan kashi 81 cikin 100. (Ibrahim)