logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a dauki matakin da zai daidaita halin da ake ciki a Ukraine

2022-03-28 20:08:12 CRI

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi kira ga dukkan bangarori, da su dauki matakan da suka dace, don magance halin da ake ciki a kasar Ukraine, da inganta tattaunawa a maimakon kara ruruta wutar rikici.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na yau da kullun Litinin din nan, bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin "ba zai ci gaba da zama a kan mulki ba."

Wang Wenbin ya kuma bayyana cewa, tarihi ya sha tabbatar da cewa, takunkumi bai taba magance matsalolin ba, sai ma ya haifar da wasu sabbi. (Ibrahim)