logo

HAUSA

Rasha da Ukraine za su shiga sabon zagayen tattaunawar zaman lafiya

2022-03-28 10:43:55 CMG Hausa

Wakilan kasashen Rasha da Ukraine za su shiga zabon zagayen tattaunawar zaman lafiya gaba da gaba, tsakanin 29 zuwa 30 ga watan Maris, shugaban tawagar wakilan tattaunawar na bangaren Rasha, Vladimir Medinsky ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Medinsky ya bayyana ta kafar telegram cewa, bayan gudanar da zagaye na baya bayan nan na tattaunawar da bangaren Ukraine ta kafar bidiyo, sakamakon hakan, an yanke shawarar shirya tattaunawar gaba da gaba a ranar 29 zuwa 30 ga watan Maris.

Bugu da kari, David Arakhamia, mamban tawagar wakilan kasar Ukraine ya bayyana cewa, za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar kai tsaye a Turkiyya tsakanin 28 zuwa 30 ga watan Maris.

Tun daga ranar 28 ga watan Fabrairu, Rasha da Ukraine, sun gudanar da zagaye uku na tattaunawar zaman lafiya gaba da gaba, da kuma jerin wasu tattaunawar ta kafar intanet, inda aka gaza cimma babbar matsaya.

Sabon zagayen tattaunawar zai gudana ne bayan dakarun sojojin Rasha sun sanar a ranar Juma’a cewa, sun kammala dukkan muhimmin zagayen farko na ayyukan soji na musamman da Rasha ta kaddamar a Ukraine. (Ahmad)