logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu gaggarumin ci gaba wajen kare fadamu

2022-03-28 13:50:54 CRI

Alkaluman da hukumar kula da dazuka da filayen ciyayi ta kasar Sin ta samar sun yi nuni da cewa, kawo yanzu akwai muhimman sassan fadamu 64 a kasar, wadanda fadinsu ya kai eka miliyan 7.32.

Sakamakon binciken da aka gudanar a shekarar 2021 ya nuna cewa, fadin fadamu ya karu a kasar Sin, kuma an kiyaye ruwan da ake da shi a fadamun ko ma ya karu kadan, kana ruwan ya kara ingantuwa, baya ga mabambantan halittun da ke rayuwa a fadamu da su ma suka karu, wadanda suka shaida ci gaban da aka samu wajen kare fadamun.

Wani jami'in sashen kula da fadamu na hukumar kula da dazuka da filayen ciyayi tna kasar Sin ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun da suka gabata, gaba daya gwamnatin kasar Sin ta zuba kudin Sin yuan biliyan 19.8 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.1) ga wasu ayyuka sama da 4100 na gyara fadamu. (Lubabatu)