logo

HAUSA

Mataimakin firaministan Sin: Akwai bukatar karfafa nasarorin da aka cimma na yaki da fatara

2022-03-28 14:36:58 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua ya yi kira da a kara kokarin karfafa nasarorin da aka cimma na yaki da talauci da tabbatar da aiwatar da manufofin da aka tsara na farfado da yankunan karkara domin samun moriya mai kwari.

Hu Chunhua ya bayyana haka ne yayin wani taro a Qujing dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin.

A cewarsa, ya kamata a kara kudin shigar mutanen da aka fitar daga kangin talauci ya zama jigon aikin, yana mai kira da samar da guraben aikin yi da inganta raya masana’antu da kuma kyautata tsarin rayuwar jama’a.

Ya kara da cewa, ya kamata babban burin da za a mayar da hankali kan sa ya zama gaggauta ci gaban gundumomin da suka fatattaki talauci da kara mayar da hankali kan masana’antun yankunan karkara. Yana mai cewa, ya kamata su kuma yankunan da suka samu ci gaba, su kara zage damtse.

Bugu da kari, mataimakin firaministan ya ce ya kamata a ingiza farfado da yankunan karkara, kana ya kamata shirin ya shafi dukkan manoma, tare da mayar da hankali kan muhimman bangarori 5 na masana’antu da al’adu da basira da kiyaye muhalli da shirye-shirye. (Fa’iza Mustapha)