logo

HAUSA

Kwarewar Sin Wajen Kawar Da Talauci Zai Amfana Wa Afirka Wajen Neman Samun Ci Gaba Mai Dorewa

2022-03-28 19:59:09 CRI

Afirka, nahiya ce wadda ke da albarkatun ma’adinai da yawan jama’a da kuma babbar kasuwa, amma ita ce nahiya mafi fama da talauci a duniya. Kawararru daga kasashen Afirka sun nuna cewa, nahiyar za ta iya koyi da kwarewar Sin wajen kawar da talauci, kuma sannu a hankali za ta kai ga cimma muradun ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.

Masani kan harkokin kasa da kasa na Kenya, Cavince Adhere ya nuna cewa, Sin tana dora muhimmanci kan kawar da talauci a cikin yankunan karkara, kuma ta cimma maradun neman ci gaba mai dorewa na MDD ta hanyar amfani da aikin gona na zamanin, ”Wannan wata fasaha ce mai amfani da za ta taimakawa Kenya da kuma sauran kasashe masu tasowa. ”

Paul Zilungisele Tembe, babban manazarci na sashen nazarin harkokin shugabanci na jami’ar Thabo Mebki dake Afirka ta Kudu, ya ce, yadda Sin ta mayar da harkokin jama’a a gaban kome a lokacin da take kokarin kawar da kangin talauci, da kuma neman samun bunkasuwa ta bai daya, kana dukkan ’yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin suna sahun gaba wajen aiwatar da kudurorin da jam’iyyar da gwamnatin kasar Sin suka tsara.

A yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar Sin da Afirka (FOCAC) da aka yi a karshen shekarar 2021, bangaren Sin ya sanar da cewa, zai aiwatar da “ayyuka guda tara”, wadanda suka shafi fannonin kawar da talauci da moriyar manoma da neman samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma kyautata karfin shugabanci da makamatansu. Wadannan ayyuka 9 sun samu maraba da amincewa sosai daga wajen abokan hulda na Afirka. Shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya jinjinawa manufar da Sin ta dauka, inda ya nuna matukar sha’awa kan yadda kasar Sin take kawar da talauci da kuma samar da fasahohin zamani ga Afirka. (Mai Fassarawa: Safiyah Ma)