logo

HAUSA

An gano akwatin tattara bayanai na biyu na jirgin saman MU5735 na kasar Sin da yayi hadari

2022-03-27 15:32:59 CMG Hausa


 

A yau Lahadi , an gano akwatin tattara bayanai na biyu na jirgin saman fasinja na MU5735 na kamfanin jirgin saman kasar Sin wato China Eastern Airlines.

Jirgin saman na MU5735, wanda ya taso daga birnin Kunming zuwa Guangzhou, duk birane ne na kasar Sin, yayi hadari da yammacin ranar Litinin a yakin Guangxi Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. Dukkan mutanen dake cikin jirgin su 132 sun mutu, kamar yadda jami’an aikin ceto suka tabbatar da hakan a ranar Asabar.

An bada sanarwar ne kwanaki shida bayan gudanar da cikakken bincike a wajen da hadarin ya faru, da kuma duba kyamarorin bincike, da sauran na’urorin dake lura da taswirar yankuna. Kawo yanzu, an gano kwayoyin halittun mutane 120 da hadarin ya rutsa dasu ta hanyar gwaje-gwajen.

An gano akwatin tattara bayanai na farko ne a ranar Laraba, kuma ana ci gaba da gudanar d ayyukan kwashe bayanan daga cikin akwatin farkon.

Za a gabatar da rahoton binciken farko ga hukumar kula da sifurin jiragen sama ta kasa da kasa cikin kwanaki 30, kamar yadda shugaban cibiyar binciken hadduran jiragen sama na kasar Sin CAAC, Mao Yanfeng ya bayyana a ranar Juma’a.(Ahmad)