logo

HAUSA

An kaddamar da gadar Foundiougne da kamfanin Sin ya gina a Senegal

2022-03-27 16:00:27 CRI

Jiya Asabar 26 ga wata, shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya halarci bikin kaddamar da babbar gadar Foundiougne da kamfanin kasar Sin ya gina ta hanyar rancen kudin da kasar ta nema daga kasar Sin.

Kamfanin kasar Sin ya fara aikin gina gadar tun shekaru uku da suka gabata, yanzu haka gadar ta fara aiki a hukumance. Shugaban kasar Senegal da magajin birnin Foundiougne da jakadan kasar Sin dake kasar da wasu wakilan kamfanin kasar Sin sun halarci bikin, inda shugaban kasar Sall ya yanka kyalle domin bude gadar.

Babbar gadar mai tsayin mita 1600 tana birnin Foundiougne dake yamma maso tsakiyar kasar Senegal, wadda ke ketare kogin Saloum, a halin yanzu gadar ta kasance mafi tsayi a kasar wadda ke ketaren kogi, kuma aikin gina gadar daya ne daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa bisa “shirin farfado da Senegal”, kana wani kokari ne da kasar Sin ke yi domin tabbatar da ayyukan hadin gwiwa goma karkashin huldar Sin da kasashen Afirka. (Jamila)