logo

HAUSA

Ci Gaban Dake Mayar Da Hankali Kan Jama’a Na Da Muhimmanci Ga Kare Hakkokinsu

2022-03-26 16:14:16 CMG Hausa

Zaunannen jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, shi ne ya kamata ya kasance jigon dabarun kawar da rashin daidaito a tsakanin al’ummun duniya.

Chen Xu, wanda ya bayyana haka ga taro na 49 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD a Geneva, ya ce annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya da ci gaban rayuwar jama’a, musammam ma rayuwar jama’ar kasashe masu tasowa. Wannan ya ta’azzara rashin daidaito da haifar da kalubaloli masu tsanani ga ci gaban duniya. Don haka, ya kamata kasashe su mayar da hankali wajen inganta ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, musammam magance rashin daidaito ta fannin ci gaba a tsakanin kasashe, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba.

Ya kara da cewa, jigon demokuradiyyar kasa ya dogara ne da ko al’ummarta ne ke kan gaba a dukkan manufofinta, haka kuma ko tana warware matsalolin da suke fuskanta ko a’a.

Jakadan na kasar Sin ya bayyana cewa, yayatawa da kare demokuradiyya da hakkokin jama’a, hakki ne na bai daya da ya rataya kan kasa da kasa. Kana bai kamata ya zama wata hanya ta matsawa kasashe lamba ba.

Bugu da kari, ya ce duk wata kasa dake keta ka’idojin demokuradiyya da yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na kasashe masu cikakken ‘yanci, bisa fakewa da kare demokuradiyya da hakkokin jama’a, wadda kuma ke yunkurin kakaba nata tsarin demokuradiyya kan wasu, to ta yi hannun riga da ainihin ma’anar demokuradiyya. (Fa’iza Mustapha)