logo

HAUSA

Sin Da India Sun Amince Da Karfafa Tuntubar Juna Domin Inganta Huldarsu

2022-03-26 15:57:49 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi dake ziyara a kasar India, tare da takwaransa na kasar Subrahmanyam Jaishankar, sun amince su karfafa tuntubar juna a tsakanin kasashensu, domin kara raya dangantakar dake tsakaninsu.

Yayin tattaunawar da ministocin biyu suka yi a New Delhi, babban birnin India, Wang Yi ya ce kasashen Sin da India da suka kasance makwabtan juna dake da jimilar al’umma biliyan 2.8, na da muhimmin karfi na tabbatar da daidaito tsakanin kasashen duniya da dunkulewar tattalin arzikin duniya da kasancewar mutane masu mabambantan al’adu tare da taka muhimmiyar rawa ga kyautata huldar kasa da kasa.

Wang Yi ya kara da cewa, yayin da duniya ke shiga wani yanayi na kalubale da sauye-sauye, ya kamata kasashen biyu su karfafa tuntubar juna a tsakaninsu da hada gwiwa kan matsayarsu ta kare halaltattun muradunsu da muradun bai daya na kasashe masu tasowa tare da bayar da gudunmuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankinsu da ma duniya baki daya.

A nasa bangaren, Subrahmanyam Jaishankar ya ce, India na daukar dangantakarta da Sin da muhimmanci, kuma babu abun da ya sauya daga wannan matsaya. Ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa tuntubar kasar Sin da kara aminci da juna domin farfado da dangantakarsu daga halin da take ciki nan ba da dadewa ba, da zummar ba da dama ga kulla hadin gwiwa mai kwari.

Yayin taron, bangarorin biyu sun amince cewa, farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan yankunan iyakokinsu, muradinsu ne na bai daya, da ya kamata su kula da shi ta hanyar gujewa fito na fito da daukar managartan matakan kaucewa rashin fahimta da yanke bahagun hunkunci. (Fa’iza Mustaopha)