logo

HAUSA

Sin Na Fatan Amurka Da NATO Za Su Koma Shawarwari Tare Da Rasha

2022-03-25 19:59:01 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi kira ga Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, da su hau teburin shawara tare da kasar Rasha, ko a kai ga warware ricikin Ukraine yadda ya kamata.

Da yake bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi watsi da zargin da wasu kasashe ke yi wa Sin, yana mai cewa, har kullum Sin na kan manufar riko da gaskiya da adalci ne game da batun Ukraine.

A jiya Alhamis 24 ga wata, kakakin tawagar Sin a kungiyar EU, ya ce sanarwar bayan taron NATO, ta zargi Sin ba tare da wani dalili ba, tare da dorawa kasar karan tsana da nufin muzgunawa, matakin da ko alama Sin din ba za ta amince da shi ba.

Jami’in ya ce, ya zama wajibi kasar Sin ta tunatar da NATO muhimmancin fahimtar matsayar Sin, domin kuma a ko da yaushe, Sin din na martaba ikon kasashe na mulkin kai, da ‘yanci da tsaron yankunan dukkanin kasashe, bisa ka’idar martaba dokokin MDD. Ya ce tun bayan barkewar rikicin Ukraine, bisa rungumar gaskiya da adalci, Sin ta yi aiki tukuru, wajen yayata tattaunawar wanzar da zaman lafiya, da dakatar da bude wuta, da kiyaye aukuwar mummunan yanayin jin kai a kasar.   (Saminu)