logo

HAUSA

Ghana ta sanarwar da rage kashe kudade sakamakon rashin tabbas da duniya ke fuskanta

2022-03-25 09:22:22 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar da rage karin kashi 10 cikin 100 na kudaden da take kashewa, bayan da ta rage kashi 20 cikin 100 a watan Janairu, don cike gibin kasafin kudinta na shekarar 2022, sakamakon yanayi na rashin tabbas da duniya ke fuskanta.

Ministan kudin kasar Ken Ofori-Atta ya shaidawa taron manema labarai cewa, an dauki matakin ne, domin nuna halin da tattalin arzikin duniya ke ciki a halin yanzu, ciki har da tasirin rikicin Rasha da Ukraine, da kalubalen da kasar ke fama da shi a fannin tattara kudaden shiga a cikin gida.

Ministan ya kara da cewa, yayin da muke kan aiwatar da sake duba tsarin kasafin kudi na shekarar 2022, don nuna ci gaban da ake samu a yanzu, a hannu guda kuma, gwamnati za ta kara daukar matakai, don tabbatar da cimma nasarar rage gibin kaso 7.4 cikin 100 na GDPn kasar.

Yana mai cewa, matakan sun hada da karin kashi 10 cikin 100 na rage kashe kudade na babu gaira babu dalili da ma’aikatu, da hukumomi ke yi, da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden tallafin man fetur ga duk masu rike da mukaman siyasa, da shugabannin hukumomin gwamnati daga ranar 1 ga Afrilu. (Ibrahim)