logo

HAUSA

Yadda aka bude wani sabon babi na zumuncin Sin da Afirka

2022-03-25 14:08:12 CRI

A watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasashen waje a karo na farko, bayan ya kama aiki a matsayin shugaban kasa. A yayin ziyararsa a nahiyar Afirka, ya bayyana shawarar raya dangantaka tsakanin Sin da Afirka cikin sabon zamani mai taken “Fadin gaskiya da nuna adalci, sada zumunci ba tare da boye kome ba”. Xi Jinping ya bayyana a cibiyar taro ta kasa da kasa ta Julius Nyerere dake kasar Tanzaniya cewa,"A sabon zamani da ake ciki, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta kara muhimmanci, domin Sin da Afirka suna da moriya iri daya, wannan ya sa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka."

A yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing a watan Satumba na shekarar 2018, Xi Jinping ya gabatar da manyan matakai guda 8, game da habaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wadanda suka shafi fannonin raya masana’antu da cinikayya, da harkokin kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa da sauransu. Xi ya kuma jaddada cewa, akwai fannoni guda biyar da kasar Sin ba za ta yi ba, yayin da take habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka. Ya ce, "Kasar Sin ba za ta hana kasashen Afirka zabar hanyoyin raya kansu ba. Kasar Sin ba za ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba. Kasar Sin ba za ta tilastawa kasashen Afirka yin wani abun da ba su so ba. Kasar Sin ba za ta saka wani sharadin siyasa ba a yayin da take taimakawa kasashen Afirka. Kuma, kasar Sin ba za ta nemi wata moriyar siyasa ba a yayin da take gudanar da harkokin zuba jari da sha’anin kudi a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana fatan dukkanin kasashen dake gudanar da harkoki a Afirka, za su bi irin wadannan manufofi biyar."

A ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, shugaba Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka ta kafar bidiyo, har ma ya gabatar da jawabi, inda ya gabatar da shawarar kasar Sin wajen karfafa dunkulewar al’ummun Sinawa da na Afirka, da kuma jaddada muhimmancin yin hadin gwiwa domin yaki da cutar COVID-19. Yana kuma fatan Sin da Afirka za su zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata, da inganta bunkasuwar kasashen ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma kare yanayin adalci a duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)