logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a yi watsi da gabatar da labarai marasa tushe a fannin kare hakkin dan Adam

2022-03-25 21:17:44 CRI

Zaunannen wakilin Sin a MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Geneva Jiang Duan, ya yi jawabi a madadin wakilan kasashe fiye da 20, da suke da ra’ayi kusan iri daya da kasar Sin, a gun taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 49,

Cikin jawabin da ya gabatar a jiya Alhamis, Jiang ya bayyana baiken yadda wasu kasashe ke amfani da dalilin kare hakkin dan Adam, wajen gabatar da labarai marasa tushe, da zargin sauran kasashe, tare da yin kira ga bangarori daban daban, da su hada kai don kin amincewa da jita-jita maras tushe. (Zainab)