logo

HAUSA

Malawi ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta BRI da kasar Sin

2022-03-24 10:43:22 CMG Hausa

Jiya ne, kasar Malawi ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Sin kan hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” a birnin Lilongwe, inda ta zama kasa ta baya bayan nan da ta shiga wannan shawara. 

A yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, ministar harkokin wajen Malawi Nancy Tembo ta yi nuni da cewa, shiga shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)” da kasar ta yi, zai samar da wani sabon kuzari ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. 

Ta kara da cewa, gwamnatin Malawi tana ci gaba da jajircewa, wajen karfafa dangantakarta da Jamhuriyar Jama'ar Sin a matakin kasashen biyu da kuma bangarori daban-daban kan batutuwan da suka shafi moriyar juna.

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin dake Malawi Liu Hongyang ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta hada shawarar “ziri daya da hanya daya”, da shirin raya kasa na kasar Malawi nan da shekarar 2063, da kuma ba da gudummawa ga gina kasar Malawi mai wadata da dogaro da kai.

Ya zuwa yanzu dai, sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 170, sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)” da kasar Sin. (Ibrahim Yaya)