logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Iran ya ce ana daf da kammala yarjejeniyar JCPOA

2022-03-24 11:29:36 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Iran wanda ke ziyarar aiki kasar Sham, Hossein Amir Abdollahian, ya bayyana cewa, kasarsa tana kusa da cimma yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, wacce aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA).

Amir Abdollahian ya fadawa ’yan jaridu bayan kammala tattaunawa da takwaransa na kasar Sham Faisal Mekdad, da sauran manyan jami’ai a Damascus cewa, sun yi amanna fiye da kowane lokaci, suna kusa da cimma matsaya kan yarjejeniyar da kuma kammala yarjejeniyar a Vienna.

Ya ce, “idan Amurka ta amince bisa gaskiya, kuma ta aiwatar da batun yadda ya kamata, to a shirye muke mu bayyanawa duniya wannan yarjejeniyar.”

Ya ce, “mun gabatar da bukatunmu na karshe ga Amurka ta hanyar jami’in kungiyar tarayyar Turai EU." Ya kara da cewa, Iran ta bayyanawa Amurka a fili cewa kada ta sauya matsayinta. (Ahmad)